2 weeks ago (edited) • Ibrahim

How to Install Open Source LLMs (Like Deepseek & Qwen) for Free
— A Simple Guide Using LM Studio

Want to run powerful language models like Deepseek, Qwen, and others on your own computer—for free? Here's a step-by-step guide.

Image 1: Full view of what LM Studio looks like when everything is set up.
👇🏿

Step 1: Visit LM Studio
Go to:  https://lmstudio.ai/ 

Step 2: Choose Your Platform
LM Studio works on macOS, Windows, and Linux.
Pick the version for your system.

Image 3: Select the version for your computer
👇🏿

Step 3: Save the Installer
Download the file and save it somewhere easy to find.

Image 4: This is my version on Mac
👇🏿

For windows view watch this  https://youtube.com/shorts/N_1K--0DnhA 

Step 4: Install LM Studio
For macOS: Move LM Studio to your Applications folder.

For Windows: Watch the video in the LM Studio setup for guidance.

Image 5: macOS installation screen
👇🏿

Step 5: Launch LM Studio & Get Your First LLM
Open LM Studio

Click “Get Your First LLM”

LM Studio recommends a model based on your computer specs

Image 6: Where you choose your first model
👇🏿

Step 6: Download a Model
Pick a model (like Qwen or Deepseek), then click Download / Install.

Step 7: Start Prompting
Once it’s downloaded:
Click "Start New Chat"
You're good to go!

You’re All Set! 🤸🏿 

3 weeks ago • Ibrahim

Yawancin mutane suna fara amfani da ChatGPT ba tare da saita shi yadda ya kamata ba tun farko ba.

Hakan kamar ɗaukar sabon ma’aikaci ne ba tare da ba shi cikakken horo kan aikin sa ba.  

Ga yadda ake saita shi yadda ya dace:

- Je zuwa Settings
- Danna Personalization
- Zaɓi Custom Instructions  

Za ka ga wurare guda biyu masu mahimmanci.  

Wurin 1: Me kake so ChatGPT ya sani game da kai don inganta amsoshin sa?  

Kwafi shi wanan amsar ka rubuta masa ita ko irinta:  

Turanci👇🏿
"I am a technology consultant who trains professionals on AI, data, and digital strategy. I create content for YouTube, write for LinkedIn, teach online courses, and deliver live workshops. My audience includes mid-level professionals, educators, and startup founders.”

Hausa 👇🏿 
"Ni kwararre ne a harkar bada shawara na fasahar zamani, ina horar da kwararru kan AI, bayanai, da dabarun dijital. Ina ƙirƙirar ƙunshiya na bidiyo a YouTube, rubuce-rubuce a LinkedIn, koyar da kwasa-kwasai ta yanar gizo, da gabatar da taruka kai tsaye. Masu sauraro na sun haɗa da masu matsakaicin matsayi, malamai, da masu kafa kamfanoni."  

Wurin 2: Yaya kake so ChatGPT ya dinga amsawa?

Kwafi wanan amsar ka rubuta masa: 

Turanci👇🏿 
"Write in a confident, friendly tone. Use short paragraphs. Include clear, practical examples. Break ideas into punchy lines when needed. Don’t over-explain. When appropriate, end with a thought-provoking question.”

Hausa 👇🏿
"Ka dinga mun rubuta ne da salo mai ƙwazo da muhawara cikin raha na abokai. Ka yi amfani da jimloli gajeru. Ka bayar da misalan da ke bayyane kuma masu amfani. Idan ya cancanta, ka tsara tunaninka cikin tsari a jere. Kada ka cika ni da dogon bayani da yawa. Idan ya dace, ka ƙare da tambaya mai tunzura tunani."  

Sai ka danna Save. 

Shi ke nan.
Ka koya wa mataimakinka na dijital yadda zai dinga tunani kamar kai, ya yi magana kamar kai, kuma ya yi aiki da salo irin naka.  

Wannan shi ne ingantaccen tsari na yin amfani da ChatGPT da hikima. 

3 weeks ago • Ibrahim

Yanzu zaka iya ƙirƙirar littafin ban dariya da ake cewa—comic book kamar wannan ta hanyar amfani da sabon fasalin samar da hotuna na ChatGPT. 

ChatGPT na ci gaba da ingantuwa. 

3 weeks ago • Ibrahim

Gayyatar Zumunci da Gaisuwar Sallah—Malamiromba

Muna farin cikin gayyatar ku zuwa gaisuwar Sallah ta musamman da za mu gudanar a wannan dandali. 

Wannan taro na zumunci za a gudanar da shi kai tsaye (live) a shafinmu na Facebook, insha'Allaah.

Sunday, Mar 30  •   1:30  –  3:00  PM
Google Meet joining info
Video call link:  https://meet.google.com/qjh-gkvo-ngo 
Or dial: +1 929-276-1279 PIN: 863 740 510#

Ku kasance tare da mu don jin dadin hira, gaisuwa, da jin labaran juna. Za mu fara karfe  1:30  na rana a yau insha'Allaah, don haka kada ku bari a ba ku labari!

Muna fatan ganin ku a wannan muhimmin lokaci. Ku yi sharing domin sauran 'yan uwa su samu damar halarta.

Allaah ya bar zumunci! 

4 weeks ago • Ibrahim

A daily meal. 
A working laptop. 
A reason to return. 

There’s a kind of privilege we rarely name in the tech world—one that could transform the lives of almajiri children scattered across Arewa.  

It’s not just about access to devices or training. It’s about the privilege of stability:  
- A place to rest.  
- A space to think and build.  
- Reliable access to food, water, and electricity.  
- The guidance of mentors.  

For many, the barrier to learning isn’t lack of intelligence or willingness—it’s the absence of consistency.

This I think will be very impactful with  consistent school meals and support to help them continue their memorization or Islamic studies. The same principle applies to tech learning: a stable meal, a safe space, and structured mentorship can transform potential into real-world skills.  

Many almajiri children would walk miles just for an opportunity to learn. A meal could be the difference between them staying in the classroom or wandering off in search of food. If we provide the right conditions—time, tools, mentors, electricity, food, and water—we give them more than just education; we give them hope and a future.  

Tech isn’t just about innovation. It’s about inclusion. It’s about making space for those who have never been given a chance to thrive.  

Just thinking out loud, but this could be a game-changing initiative. What do you think? 

1 month ago • Ibrahim

Hausa | English 

CS50 shine kwas ɗin da na fi so idan ana batun tsarin koyon coding, ko dai ga masu farawa ko ga ƙwararru da ke son inganta iliminsu.  

Na fara ɗaukar CS50 a shekara ta 2019, inda na koyi yadda ake zubin  ƙirƙira (programming), irin yadda harshen C ke aiki, nau’ikan bayanai (data types), ayyuka (functions), abubuwa (objects), tsaruka (classes), loops, da sauransu.  

Dukkan waɗannan abubuwan sun taimaka min wajen fahimtar yadda ake gina manhajoji da shafukan yanar gizo daga baya, wanda hakan ya kai ni ga koyar da Python ga ƴan makaranta a 2021.  

Ka taɓa gwadawa kuwa?  

Idan kana son samun hanyoyin haɗin CS5O, ka rubuta "HARVARD"  a sashen sharhi.

Malamiromba Ltd Muna da aji Online da Physical a Kano. 

_______________
CS50 is my favorite course when it comes to learning coding, whether you’re a beginner or an expert looking to enhance your knowledge.

I first took CS50 in 2019, where I learned about programming, including how the C language works, data types, functions, objects, classes, loops, and more.

All these topics helped me understand how to build applications and websites later, which eventually led me to teach Python to secondary students in 2021.

Have you ever tried it?

If you’d like to get the CS50 links, type "HARVARD" in the comment section.

MALAMIROMBA LTD  – We offer both online and physical classes in Kano.

 #CS50x   #Coding   #Havard   #Cs50   #Freecourses   #programmers   #100dayofcode   #softwareengineer 

1 month ago • Ibrahim

Ka san 2FA (Two-Factor Authentication) ?

Wata hanya ce na kara tsaro ga asusunka na yanar gizo. Bayan ka saka kalmar sirri—Password, sai an bukaci karin tabbaci, kamar lambar da za a turo maka a waya—SMS, app na authentication, ko kuma kayi amfani da yatsa—fingerprint ko fuska—face verification. 

Wannan yana hana masu kutse shiga asusunka ko da sun san kalmar sirrinka. 

1 month ago • Ibrahim

English | Hausa 

Babu wanda ka sani, ko wani a wannan zamani da bai taɓa amfani da AI ba.  

Domin AI na ko’ina, musamman a wayoyin mu na hannu.  

A wane lokaci kake tunanin ka fara amfani da Ƙirƙirarriyar Basira (AI)?  

An ƙirƙiri Google a 1998, kuma gaba ɗayan Google, AI ne. (Wasu za su ce lissafin—mathematical model ba AI bane, amma sun manta shi kansa AI lissafin—Mathematical model ne!)  

Yau, duk muna amfani da AI a cikin wayoyin mu—kawai dai kafin wanan lokaci, ba mu san cewa AI ne muke amfani da shi ba, tunanin mu "fasaha—technology " ce kawai.  
_______

There is no one you know, or anyone in this world in this current century, who has never used AI before.  

This is because AI is everywhere, especially in our mobile phones.  

When do you think you first used Artificial Intelligence?  

Google was invented in 1998, and Google is entirely AI. (Some may argue that it's just a mathematical model, but AI itself is a mathematical model too.)  

Today, we are all using AI on our mobile phones—it’s just that, before now, we didn’t realize it was AI. We simply thought it was just "technology." 

1 month ago (edited) • Ibrahim

Ma’anar AI (Ƙirƙirarriyar Basira) ta sauya sosai tun bayan yawaitar buɗaɗɗun damar gina su, inda ƙirƙire-ƙirƙire suka ƙaru.  

Iya ambaton “ChatGPT” kaɗai na iya tayar da muhawara mai zafi tsakanin mutane a kan tasirin da AI ke ƙara samu a rayuwarmu ta yau da kullum.

Me ka sani game da AI ?
Wani amfani ka kiyaye zai maka ko yake maka ?
Ka san ethical applications ɗinsa kuwa ?, ko kaima kana daga cikin masu shuka ba tare da nazarin irin ba?
________

The definition of AI has dramatically changed since the recent avalanche of open source libraries and applications. 

Just mentioning “ChatGPT” can trigger passionate debate about the emerging power of AI in our daily lives.

What do you know about AI?  
What benefit have you observed it gives you or is giving you?  
Do you know its ethical applications? Or are you also among those who plant without examining the seed?

Domin samun horon amfanin da AI (AI literacy) ka kallon jerin bidiyoyin nan nawa 👇🏿👇🏿👇🏿

 https://youtube.com/playlist?list=PLT... 

1 month ago • Ibrahim

Tambaya a buɗe!

Sannu dai Malamiromba, kwanakinnan ina ta ƙoƙarin shiga fagen fasaha don samun kuɗi. Ina sha’awar kyamarori, don haka na karkata zuwa ga zamowa mai ƙirƙirar ƙunshiya (content creation). 

Amma ina son in sani, shin ƙirƙirar ƙunshiya shima fage ne na fasaha? Zan iya kiran kaina da ƴar fasaha idan ni a irin wannan fagen nake? Sannan wani fagen kuma da nake fatan shiga ciki shi ne fannin sarrafa ayyuka (project management) ko da cewa wancan fagen bai tabbata ba. 

Menene shawararka? Hajara, 23.

Barkanmu dai Hajara, (Mai shekaru 23)

Tabbas ƙirƙirar ƙunshiya fage ne na fasaha! Duk da yake ba kodin bane ko nazarin bayanai (data analysis), yana da muhimmanci ga "kafofin watsa labarai na dijital" ko "fasahar aikace." Lokacin da kike ƙirƙirar ƙunshiya, kina aikine da manhajoji, dandamalai, da kayan aikin fasaha - wannan duk fasaha ce. Don haka, eh, ke ƴar fasaha ce!

Ki yi la'akari da wannan:

Fasahar aikace: ta danganci amfani da manhajoji na fasaha da dandamali don ƙirƙira da rarraba ƙunshiya (content).

Kafofin watsa labarai na Dijital: su jigo ne na hanyoyin sadarwar zamani, wanda suka dogara da fasaha sosai.

To kinga kuwa, duk fannonin a zagaye suke da juna. Game da shirinki na koyon sarrafa ayyuka a madadin ƙirƙirar ƙunshiya, wannan kyakkyawan ra'ayi ne. Ki fara koyon shi tun yanzu, ba sai daga baya ba. Zai zamo cikamakon ƙwarewarki a ƙirƙirar ƙunshiya sosai. Kinga sai ki zamo ƙwararriya a fannin sarrafa ƙunshe-ƙunshe (Contents project manager). Yana da kyau ki tallata ƙwarewarki ga duniya yayin da kike koyon.

A ƙarshe, ki tabbatar cewa kina ci gaba koyaushe, ki riƙa bibiyar sabbin abubuwan da ke faruwa a fagen fasaha kuma ki riƙa amfanar da masu bibiyarki. Ina miki fatan alkhairi Hajara.

Kuna da tambayar da take cinku? Ku jefo ta nan  https://forms.gle/a7MDeBDXJYuoJ81p6 

________
Translated by Abdulhadi N. Bashir